Nigerian news All categories All tags
PDP da wa’azi kan rashawa tamkar Karuwa mai wa’azi kan kamun kai ce - APC

PDP da wa’azi kan rashawa tamkar Karuwa mai wa’azi kan kamun kai ce - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ba tada kunya da hurumin magana kan yaki da rashawa saboda tamkar karuwa mai wa’azin kamun kai ne.

Kakakin jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya saki a yau Alhamis domin raddi ga sukar da PDP ta saki kan zaben kwamred Adams Oshiomole a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Bayan zaben Oshiomole, PDP tace: “Ana sanar da yan Najeriya cewa wasu yan jam’iyyar da ake so musamman shugabansu, mutane ne masu kashi a gindi amma an basu shugabanci domin rufe musu baki shugaba Buhari ya samu tikitin sake takara.

“Duniya ta shaida yadda jami’an tsaro da yan baranda suka mutuncin wasu yayan jam’iyyar da suka nuna rashin yarda “

KU KARANTA: An sake daga karar Maryam Sanda da watanni 3

Amma a raddin APC, kakakin jam’iyyar yace PDP a bayan kwace mulki daga hannunta shekaru uku yanzu, na kara bayyana jahilcinsu a fili kuma yadda sukeyi zai yi wuya yan Najeriya su musu gafarar da suke nema.

Yace: “Amma mun san matsalan PDP. Sun kidime ne da kwamred Adams Oshiomole. Sun san ba zai raga musu ba ko kadan.”

PDP da wa’azi kan rashawa tamkar Karuwa mai wa’azi kan kamun kai ce - APC

PDP da wa’azi kan rashawa tamkar Karuwa mai wa’azi kan kamun kai ce - APC

Jam’iyyar APC ta zabi sabbin shugabaninta ne a karshen makon da ya gabata bayan kare wa’addin tsaffin shugabannin na shekara hudu a taron gangamin da aka gabatar ranan 23 ga watan Yuni, 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel