Nigerian news All categories All tags
Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna

- Da sauran rina a kaba kan sha'anin masu garkuwa da mutane a Kaduna

- A cikin sati nan ma dai an samo rahotan sace wasu mutane biyu a jihar

- Kuma har ya zuwa yanzu ba'a samu rahotan sakinsu ba

A ranar Labara da daddare ne aka sace wasu mutune guda biyu akan titin filin jirgin saman jihar Kaduna kamar yadda wata majiya ta rawaito.

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna

Majiyar jaridar Daily Nigerian bayyana cewa mutum biyun (Dan uwa da kanwarsa) suna kan hanyarsu ta dawowa daga tashar jirgin sama a lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe 8pm na dare.

"Dan uwan ya tafi dauko yar uwarsa ne daga tashar jirgin sama akan hanyarsu da dawowa sai masu garkuwa da mutane suka tare musu hanya."

KU KARANTA: Ba labari! Wani tsohon Soja ya harbe kansa har lahira

"Shugaban hukumar yan sanda na jihar Kaduna ya shaida cewa duk mutanen da suke amfani da hanyar filin jirgin sama na Kaduna ya kamata suke zama cikin shiri da bude ido sosai domin bayyana duk wani wanda basu yarda da shi ba, don akwai Baragurbi sosai akan hanya", cewar kakakin hukumar yan sanda na jihar Kaduna Muktar Aliyu.

Biyo bayan wannan lamari yanzu haka hukumar ta saka jami'anta akan hanyar zuwa titin jirgin saman da kuma cikin tashar tashi da saukar jirage na Kaduna domin tabbatar da tsaro ga al'umma.

Hukumar ta tabbatar da jama'a cewa zata cigaba da kokari wajen karewa mutane dukiyoyinsu da kuma lafiyarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel