Nigerian news All categories All tags
Bankin Duniya zai bayar da bashin $2.1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka 7 a Najeriya

Bankin Duniya zai bayar da bashin $2.1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka 7 a Najeriya

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, Bankin Duniya ya bayar da sanarwa ta lamunin bashi na Dalar Amurka Biliyan 2.1 domin gudanar da wasu muhimman ayyuka bakwai a kasar nan ta Najeriya.

Cikin wata sanarwar ranar Alhamis din da ta gabata a garin Abuja da ta bayyana cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne aka bayar da amincewar wannan bashi a birnin Washington na kasar Amurka domin gudanar da wasu muhimman ayyuka bakwai a kasar nan.

Rahotanni sun cewa, babban bankin zai bayar da wannan bashi ne domin tallafawa Najeriya aiwatar da ayyukan da suka hadar da harkokin abinci, wutar lantarki, kasafin kudi na kudaden shiga, kawar da cutar shan inna, inganta tattalin arzikin Mata, bunkasa tattali da kiyasi kasa da kuma magance zaizayar kasa.

Bankin Duniya zai bayar da bashin $2.1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka 7 a Najeriya

Bankin Duniya zai bayar da bashin $2.1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka 7 a Najeriya

Daraktan Bankin na duniya reshen Najeriya, Rachid Benmessaoud, shine ya bayyana hakan da cewar akwai bukatar bunkasa muhimmin ginshiƙi na tattalin arzikin kasar nan da kawo ci gaba a cikin ta.

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ci gaba ta Duniya, ita tayi ruwa da tsaki kan wannan lamari domin tallafawa Najeriya ta fuskar bunkasar tattallin arziki.

DUBA WANNAN: Fasakauri: Hukumar Kastam ta cafke Mutane 8, ta tara N9.4bn cikin watanni Shida

Najeriya ta samu zagon kasa ta fuskar ci gaban ta sakamakon matsain tattalin arziki da fuskanta tun gabanin watan Satumba na shekarar 2016 da ta gabataa sanadiyar dogaro da kudaden shiga da take samu wajen sayar da man fetur da ma'adanan sa.

Gwamnatin Najeriya tana da kyakkyawan zato tare da fata nagari wajen bunkasar tattalin arzikin ta da kaso 7 cikin 100 zuwa shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel