Nigerian news All categories All tags
An cafke mutane biyu da ake zargi da tayar da bam a gidan tsohon Minista

An cafke mutane biyu da ake zargi da tayar da bam a gidan tsohon Minista

Hukumar Yan sanda reshen jihar Enugu ta sanar da cewa ta kama mutane biyu da ke da hannu cikin tayar da bam a gidan Cif John Nnia Nwodo, tsohon ministan sadarwa kuma shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo.

Kwamishinan Yan sandan jihar, Mr. Mohammed Danmallam ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis a Enugu.

A ranar 29 ga watan Afrilun 2018 ne dai wasu bata gari suka dasa bama-bamai kuma suka tayar da su a gidan tsohon ministan da ke karamar hukumar Igbo-Ettit na jihar Enugu.

An kama mutane biyu bayan tashin bam a gidan tsohon Minista

An kama mutane biyu bayan tashin bam a gidan tsohon Minista

Dan mallam ya ce jami'an yan sandan sunyi amfani da bayyanan sirri da aka tattaro ne wajen gano wadanda suka aikata barnar.

KU KARANTA: Zargin rashawa: Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

"Bayan harin da su kayi, sun cigaba da aika wa Nwodo sakonin text inda suka rika yi masa barazana tare da siffanta shi da kalamai marasa dadi.

"A yayin da muke gudanar da binciken mu, mun gano cewa ashe mambobin haramtaciyar kungiyar IPOB ne," inji shi.

Kwamishinan kuma ya ce hukumar ta kama wani wanda ake zargin ya sace wata karamar yarinya kuma ya yi mata fyade kana daga baya ya kashe ta. Yarinyar mai shekaru 15 a duniya dai dalibar makarantar sakandire ce da ke SS II.

Ya ce wanda ake zargin ya sace yarinyar ne a ranar 13 ga watan Mayu kuma ya birne ta kabari mara zurfi bayan ya kashe ta.

"Wanda ake zargi da satar mutanen da kisa dan asalin kauyen Aninri ne," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel