Ku daina bawa 'yan daba makamai - IG ya gargadi 'yan siyasa

Ku daina bawa 'yan daba makamai - IG ya gargadi 'yan siyasa

Sufeta Janar na Yan sandan Najeriya Ibrahim idris ya tabbatar wa hukumar zabe mai zaman kanta INEC cewa za'a samar da cikaken tsaro da yan sandan sintiri da helicofta yayin babban zaben kasa na shekarar 2019.

Idris ya bayar da wannan tabbacin ne a Legas yayin wani taron da aka shirya saboda tsara yadda za'a rabar da kayayakin zaben da hukumar INEC za ta gudanar a 2019.

Sufeta Janar din kuma ya shawarci yan siyasa su dena bawa yan daba makamai kuma su dena daukan siyasa harkar 'a mutu ko ayi rai. "Ya kuma kamata yan siyasa su dena yadda kalaman idan har ana son gudanar da zabe cikin zaman lafiya a 2019."

Ku daina bawa 'yan daba makamai - IG ya gargadi 'yan siyasa

Ku daina bawa 'yan daba makamai - IG ya gargadi 'yan siyasa

A cewarsa idan yan siyasa yan siyasa su kayi biyaya ga dokokin zabe, hukumar yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su tabbatar da cewa anyi zaben cikin zaman lafiya.

KU KARANTA: Zargin rashawa: Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

Ya kuma ce duk wani dan siyasa da aka kama yana bawa masa kada kuri'a cin hanci a zaben Ekiti da Osun da babban zaben 2019 sai fuskanci fushin hukuma.

A zaben jihar Ekiti da za'a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli, shugaban yan sandan ya ce za'a samar da yan sanda 16,186 ciki har da jami'an yan sanda na musamman.

A bangarensa, shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ya ce samar da kayayakin zaben a kan lokaci shine sai tabbatar da samun nasara a babban zaben na 2019, ya kuma ce taron bitar shine horoswa na karshe da hukumar za tayi kafin zaben.

A cewarsa, rashin samar da kayayakin zaben a kan lokaci a wuraren da ya kamata take hakkin masu zabe ne saboda ya zama dole hukumar tayi shiri na musamman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel