Badakalar Abacha: Kudin ku ya kare - Kasar switherlanda ta sanar da Najeriya

Badakalar Abacha: Kudin ku ya kare - Kasar switherlanda ta sanar da Najeriya

Bayan dawowa da Najeriya ragowar dalar Amurka $321 daga cikin kudin da tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Marigayi Janar sani Abacha, ya wawure ya boye a Switherland lokacin da yake kan mulki, jakadan kasar a Najeriya, Eric Mayoraz, ya sanar da cewar babu ragowar wasu kudi kuma da Abacha ya boye a kasar.

Jakada Mayoraz ya bayyana cewar kasar sa ta Switherland, ya zuwa yanzu, ta dawowa da Najeriya dukkan kudin da tsohon shugaba Abacha ya boye a kasar.

Jaridar Vanguard ta rawait cewar, jakada Mayoraz ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya domin bitar dawowa Najeriya kadarorinta da dukiyar da masu mulki suka wawura tare da taskance su a kasashen ketare.

Badakalar Abacha: Kudin ku ya kare - Kasar switherlanda ta sanar da Najeriya

Sani Abacha

Jakadan ya bayyana cewar, a baya gwamnatin Switherland ta dawowa da Najeriya dalar Amurka miliyan $752 daga cikinjimillar kudin da Abacha da iyalinsa suka boye a bankunan kasar, kafin dalar Amurka miliyan $321 da kasar ta dawo dawo da su kwanakin baya.

DUBA WANNAN: Tsohuwar minista ta amayar da miliyoyin kudin makamai da ta hadiya bayan ta ji matsar EFCC

Kazalika ya bayyana cewar, sabbin dokoki da yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kasashen ketare, zai yi wuya wani shugaba ya saci kudi kuma ya samu damar boye su a bankunan kasashen Turai..

Marigayi Janar Sani Abacha ya shugabanci Najeria a mulkin soji daga shekarar 1994 zuwa 1997, shekarar da ya mutu. Amma shekaru 11 bayan mutuwar sa, gwamnatin Najeriya na cigaba da karbar kudin da ya kwasa daga asusun gwamnati tare da jibge su a bankunan kasar Switherland a asusun 'ya'yansa na cikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel