Nigerian news All categories All tags
Fasakauri: Hukumar Kastam ta cafke Mutane 8, ta tara N9.4bn cikin watanni Shida

Fasakauri: Hukumar Kastam ta cafke Mutane 8, ta tara N9.4bn cikin watanni Shida

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya bayyana mun samu rahoton cewa, hukumar kastam reshen jihar Oyo da Ogun, ta tarawa gwamnatin tarayya kudaden shiga na kimanin Naira biliyan 9.4 a tsakanin watan Janairu da Mayun 2018.

Shugaban hukumar reshen Kwanturola Christopher Odibu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Shelkwatar ta dake birnin Ibadan, dangane da cafke wasu kayan fasakauri na kimanin Naira Miliyan 50.6.

Kwanturola Odibu yake cewa, idan aka kwantata da naira biliyan 7.2 da hukumar ta samar a shekarar da ta gabata, hakan ya bayyana lallai an samu karuwar adadin kudaden masu yawa a reshen hukumar.

Fasakauri: Hukumar Kastam ta cafke Mutane 8, ta tara N9.4bn cikin watanni Shida

Fasakauri: Hukumar Kastam ta cafke Mutane 8, ta tara N9.4bn cikin watanni Shida

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta samu nasarar dakile wasu kayan fasakauri da suka hadar da; Motoci na alfarma, shinkafa da kuma Man gyada da sukari na tarin dukiya mai dumbin yawa.

DUBA WANNAN: Buhari yana yiwa ta'addancin Makiyaya rikon Sakainar Kashi - Soyinka

Babban jami'in ya ci gaba da cewa, hukumar ta samu nasarar dakile wannan kayayyakin fasakauri musamman akan babbar hanyar Saki dake yankin Oke a gabar jihar Ogun da Oyo.

Ya kara da cewa, a yayin haka kuma hukumar ta samu nasarar cafke wasu mutane 8 bisa aikata laifin Sumoga da a halin suke gaban Kuliya inda take gudanar da shari'a a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel