Nigerian news All categories All tags
Idon wani dan basajan EFCC ya raina fata, ya samu hukunci mai tsanani a kotu

Idon wani dan basajan EFCC ya raina fata, ya samu hukunci mai tsanani a kotu

- Asirin wani mai amfani da sunan gumin EFCC yana karbar kudi ya tonu

- Kuma har ya fuskanci hukunci mai tsanani bayan da yayi ta magiyar beli alkali yaki

- Mai shari'ar ya ce yana so ne ya dandana kudarsa, don hakan ya zama darasi ga 'yan baya

A yau Alhamis wata babbar kotu dake zamanta a Benin, ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna AKeju Isaac hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari, sakamakon kama shi da laifin yin sojan gona a matsayin jami’in hukumar EFCC.

Idon wani dan basajan EFCC ya raina fata, ya samu hukunci mai tsanani a kotu

Idon wani dan basajan EFCC ya raina fata, ya samu hukunci mai tsanani a kotu

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Esohe Ikponwen ya bayyana cewa kotun ta kama shi da laifuka biyun da ake tuhumarsu da shi na hadin baki da kuma karbar kudin mutane a matsayin sojan gona.

A cewar alkalin wannan babban laifi ne don haka dole ne ya fuskanci hukunci mai tsanani domin hakan ya zama izna ga masu shirin aikata laifi irin nasa nan gaba.

Mai laifin ya roki mai shari’a Ikponwen da ya bashi zabin tara amma alkalin ya ki amincewa da wannan bukata ta shi.

KU KARANTA: Ba labari! Wani tsohon Soja ya harbe kansa har lahira

Tun farko dai Lauyan EFCC Abieuwa Usoh-Iriabe ta shaidawa kotun cewa wanda ake zargin yana nuna kansa ne a matsayin babban ma’aikacin hukumar inda har yasa aka tura masa kudi N200,000 na wani mai suna Dr Sunny Olotu babban likitan asibitin masu motsi a ka na Benin, ta cikin asusun Joseph Badmus, bayan da ya same shi ya shaida masa cewa hukumar na bincikarsa.

Kuma EFCC ta kama shi ne yayin da ya je na’urar cire kudin ta ATM, sai dai kuma tuni zakara ya bawa anihin mai asusun ajiyar sa'a ya tsere.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel