Nigerian news All categories All tags
Ana zargin APC da kashe sama da Biliyan 3.6 wajen gangamin Jam’iyyar

Ana zargin APC da kashe sama da Biliyan 3.6 wajen gangamin Jam’iyyar

Jam’iyyar adawa ta Jam’iyyar PDP ta zargi APC da kashe makudan kudi har kusan Naira Biliyan 4 wajen babban taron Jam’iyyar mai mulki da aka yi kwanan nan a Birnin Tarayya Abuja.

Ana zargin APC da kashe sama da Biliyan 3.6 wajen gangamin Jam’iyyar

Jam’iyyar PDP tana zargin APC da kashe kudi wajen gangami

PDP ya bayyana cewa sai da kowane Gwamna na Jam’iyyar APC mai mulki ya bada gudumuwar Naira Miliyan 150 wajen babban taron Jam’iyyar na kasa da aka yi. Jam’iyyar ta APC dai na da Gwamnoni 24 a fadin Kasar.

KU KARANTA: Wani Limami ya boye Kiristoci a Masallaci a Jos

Daily Trust ta bayyana cewa da aka tuntubi Jam’iyyar ta APC ta tabbatar da cewa za ta duba zargin da ake ta yadawa. Sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa Malam Bolaji Abdullahi yace za su fito su yi magana game da batun.

Jam’iyyar adawar dai tace abin kunya ne ace Gwamnonin APC sun ware makudan kudi domin taron su yayin da Ma’aikata ke fama babu albashi. Kudin da ake zargi Jam’iyyar ta kashe ya kai Naira Biliyan 3.6 inji Jam’iyyar PDP.

Bayan nan dai Jam’iyyar ta PDP ta nemi Hukumar zabe na kasa watau INEC tayi watsi da zaben Adams Kwamared Oshiomole a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC. PDP tace akwai zargin da ke kan Oshiomole a hannun Hukumar EFCC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel