Nigerian news All categories All tags
FAAC: Gwamnatin Tarayya ta tashi taro ba tare da raba albashin wannan wata ba

FAAC: Gwamnatin Tarayya ta tashi taro ba tare da raba albashin wannan wata ba

- Yunkurin raba kudin Najeriya ga kowane kaso na Gwamnati ya ci tura

- An tashi ba tare da an samu matsaya ba a taron FAAC da aka yi a jiya

- Ba mamaki dai kudin da Kamfanin NNPC ta kawowa kasar ne bai isa ba

Labari ya kai gare mu daga Jaridar Premium Times cewa an gaza cin ma matsaya a wajen taron kwamitin FACC da ke da hakkin kasafta kudin kasa da aka yi Ranar Laraba a Birnin Tarayya Abuja.

FAAC: Gwamnatin Tarayya ta tashi taro ba tare da raba albashin wannan wata ba

Ma'aikata za su iya kara kwanaki babu albashin wannan wata

Ku na sane cewa a duk karshen wata kwamishinonin kudi na Jihohi da Akanta Janar na Kasar nan kan hadu a Birnin Tarayya Abuja domin ganin yadda za a warewa Jihohi 36 na Kasar da kuma Kananan Hukumomi da Gwamnatin Tarayya kason su.

KU KARANTA: An harbe wani tsohon 'Dan takarar Gwamna a Kudu

Wannan karo an yi taro har na na kwanaki 2 amma ba a kai ga ci ba inda aka tashi cirko-cirko babu wanda ya iya yi wa ‘Yan jarida bayani a jiya, Jami’in Ma’aikatar kudi na kasar da ya kira ‘Yan jarida dai ya bayyana cewa ba za su ce komai ba a jiyan.

Jaridar ta Premium Times ta rahoto cewa kwamishinonin da sauran Ma’aikatan Gwamnatin sun yi ta kokarin gudun cin-karo da ‘Yan jarida bayan an kammala taron. Babu mamaki dai an samu matsala ne wajen kason da ya kamata kamfanin NNPC ta tara.

Shugaban Kwamishinonin kudi na Jihohin Kasar Mahmood Yunusu ya bayyana cewa za su tattauna da Iyayen gidan su watau Gwamnoninin Jihohi domin daukar mataki game da lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel