Nigerian news All categories All tags
'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

Hukumar Yan sanda reshen jihar Nasarawa ta tabbatar da kisar gilla da a kayi wa makiyaya shida tare da shanun su 150 a Akpanagya da ke karamar hukumar Keana.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sojojin da aka tura iyakar jihohin Nasarawa da Benue samar da tsaro ne suka aikata kisar.

Kakakin hukumar Yansanda na wucin gadi a jihar Nasarawa, ASP Usman Samaila ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata hirar wayar tarho da a kayi dashi a Lafiya.

'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

KU KARANTA: Mun bankado kamfanin hada magunguna mafi hatsari a duniya a kudancin Najeriya - NDLEA

"Mun samu rahoton cewa wasu sojoji daga jihar Benue sun kashe wasu mutane ake kyautata zaton makiyaya ne," inji shi.

Ya kuma kara da cewa hukumar Yan sandan ba ta da cikaken bayani kan abinda ya faru tsakanin makiyayan da sojojin.

Ciyaman din kungiyar Miyetti Allah na jihat Nasarawa, Mallam Muhammad Husseini ya nuna rashin jin dadinsa a kan lamarin kuma ya yi kira hukuma ta gudanar da bincike tare da hukunta wanda su ka aikata kisar.

A bangarensa, Kakakin hukumar sojin Najeriya, Brig. Janar Texas Chukwuma ya ce ofishin sa ba ta samu rahoton afkuwar lamarin ba a halin yanzu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel