Nigerian news All categories All tags
Buhari yana yiwa ta'addancin Makiyaya rikon Sakainar Kashi - Soyinka

Buhari yana yiwa ta'addancin Makiyaya rikon Sakainar Kashi - Soyinka

A ranar Larabar da ta gabata ne Farfesa Wole Soyinka tare da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, su ka kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari, da cewar yana yiwa ta'addaci na kashe-kashen makiyaya rikon sakainar kashi a kasar nan.

Obasanjo wanda ya kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, girman barazanar tsaro da kasar nan ke fuskanta karkashin jagorancin shugaba Buhari ta yiwa ta lokacin gwamnatin sa fintinkau.

Hakazalika Farfesa Soyinka ya jaddada cewa, kashen-kashen makiyaya a kasar nan yayi kamari ne sakamakon yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen tabuka abin kirki da zai magance hakan a kasar nan.

Obasanjo ya kalubalanci gwamnatin tarayya da ta jihohi akan su mike tsaye wajen gano tushe da ainihin dalilin da ya sanya wannan bala'i na zubar da jinin al'umma ke ci gaba da afkuwa tare da da ceto kasar nan daga mummunar matsala.

Buhari yana yiwa ta'addancin Makiyaya rikon Sakainar Kashi - Soyinka

Buhari yana yiwa ta'addancin Makiyaya rikon Sakainar Kashi - Soyinka

Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon shugaban kasar ya yarda cewa gwamnatin sa ta fuskanci makamanciyar wannan matsala sai dai ko kadan ba ta kama kafar ta ba ta fuskar munzali na girma.

Tsohon shugaban kasar ya nuna fatan cewa za a iya samun mafita don magance matsalolin da ya ba da gaisuwa ga iyalan da suka yanke wa rai.

KARANTA KUMA: Kotu ta hana bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame

Tsohon shugaban kasar ya bayyana kyakkyawan zato tare da fatan samun mafitar wannan barazana dake kalubalantar kasar nan yayin da ya kuma kara jaddada jajantawar sa ga al'umma jihar Filato musamman 'yan uwan wadanda bala'in ya shafa.

A nasa bangaren, Lalong ya yabawa Farfesa Soyinka tare da tsohon shugaba Obasanjo, inda ya bayyana cewa da sun jajanta da aikon sakon gaisuwar su ta hanyar wayar salula da hakan ma ya wadatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel