Nigerian news All categories All tags
Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari

Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Kawu Sumaila ya yi tsokaci kan lamarin kasafin kudin 2018.

A cewar Kawu, tirsasa wa shugaban kasar aka yi kan ya sanya hannu akan kasafin kudin domin shi ba haka ya so ba.

Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari

Tirsasa wa shugaban kasa aka yi ya saka hannu a kasafin kudin 2018 - Hadimin Buhari

Da aka tambayi Hon Sumaila game da korafin da akeyi cewa ba a iya aiwatar da kasafin kudin kasar nan ba ta yadda zai yi wa mutane tasiri, ya kuranta gwamnatin Buhari cewa, itace gwamnati ta farko tun bayan dawowa mulkin dimokradiyya a kasar nan a 1999 aka iya yin ayyukan dake cikin kundin kasafin kudin har kashi 75 bisa 100.

KU KARANTA KUMA: Kisan Plateau: PDP na zaman makoki na kwanaki 7

Daga yace rashin jituwa da ake samu tsakanin fannin zartarwa da majalisa siyasa ce kawai ba wani abu. Cewa idan zabe ya zo za kaga ana samun irin wadannan rashin jituwa aka-akai.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Sanatan jam’iyyar Progressives Congress (APC), Shehu Sani, yace bai kamata ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin 2018 ba.

Sani na maida martani ne ga korafin da shugaban kasar yayi akan cewa majalisar dokoki sun zaftare kasafin, wanda zai shafi manyan ayyuka da dama.

Sanatan mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin yace sanya hannun da shugaban kasar yayi akan takardun ya nuna amincewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel