Nigerian news All categories All tags
Kisan Plateau: PDP na zaman makoki na kwanaki 7

Kisan Plateau: PDP na zaman makoki na kwanaki 7

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa babban jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democratic Party, PDP ta shiga zaman makoki na kwanaki bakwai don jimamin mutanen da aka hallaka a jihar Plateau.

Jam’iyyar ta bukaci a sassauto da tutarta a dukkanin ofisoshinta da ke fadin kasar har na tsawon kwanaki bakwai da ta ayyana na zaman makokin kisan mutane sama da 200 da akayi a jihar ta Plateau.

Kkakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyanawa manema labarai cewa PDP ta bukaci al’umman jihar Plateau da su yi amfani da yancinsu na yan kasa ta hanyar kai kara kotun duniya kan gazawar gwamnati wajen kawo karshen yawan kashe-kashe a kasar.

Sai dai a lokacin da ya kai ziyarar jaje a jihar Plateau, shugaba Buhari ya kare sukarsa da 'yan adawa ke yi cewa gwamnatinsa ba ta yin komi a kashe-kashen rikicin makiyaya da manoma.

Kisan Plateau: PDP na zaman makoki na kwanaki 7

Kisan Plateau: PDP na zaman makoki na kwanaki 7

Ya ce ba a yi masa adalci game da yadda ake cewa ba ya daukar mataki kan Fulanin da ake zargi da kashe mutane saboda shi ma Bafulatani ne.

KU KARANTA KUMA: An maida Kwamishinan ‘Yan sandan Plateau kwana daya bayan cire shi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar ’Yan sandan Najeriya, ta sanar da batun mayar da Undie Adie a matsayin sa na kwamishinan ’Yan sandan Jihar Plateau, kwana daya bayan maye gurbin sa da aka yi da Ciroma.

An yi wannan sanarwar ta mayar da Adie ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuni kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel