Zargin rashawa: Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

Zargin rashawa: Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

Gwamnatin tarayya ta sake maka Sanata Akpan Bassey mai wakiltan Arewa maso gabashin Akwa Ibom a gaban kotun tarayya da ke Abuja bisa laifin bayyana kadarorin karya tare da karkatar da wasu kudade.

A karar da gwamnatin ta shigar a jiya Laraba, NAN ta ruwaito cewa gwamnatin tana zarginsa da laifuka guda biyu wanda zuka shafi cin amana, karkatar da kudin al'umma tare da makirci da amfani da matsayinsa na Sanata don aikata wasu laifufuka.

Gwamnatin tarayyar ta yi ikirarin cewa Mr Akpan ya aikata laifin bayar da bayyanan karya wanda ya ci karo da sashi 15 na dokokin da'ar ma'aikata.

Zargin rashawa: Gwamnati ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

Zargin rashawa: Gwamnati ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Sojoji sun kama 'yan leken asirin 'yan bindigan Zamfara

Babban sufritandant na kwamitin bincike na musamman na shugaban kasa, Celsus Ukpong ne ya sanya hannu kan takardar karar a madadin Attorney-Janar na kasa tare da shaidar bayyanin kadarorin da Mr. Akpan ya bayar a baya.

A takardar shaidan, Mr Akpan ya yi ikirarin cewa ba zai iya tuna adadin kudin da ya biya wajen siyan gidansa mai lamba 387 a Diplomatic Zone, Katampe Extension a Abuja ba, ya kuma ce ba zai iya tuna sunan wanda ya sayar masa a gidan ba.

Ya kuma musanta cewa shine ya mallaki wasu gidaje biyu da aka ce nasa ne duk a unguwar Diplomatic Zone a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan karar da aka shigar a kan Sanata Akpan ya kara adadin Sanatocin da gwamnati ke tuhuma da laifukan rashawa ko makamancin hakan.

Premium Times ta ruwaito cewa a halin yanzu akwai sanatoci 13 da ake tuhuma da laifukan da suka shafi rashawa ciki har da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel