Nigerian news All categories All tags
Mun bankado kamfanin hada magunguna mafi hatsari a duniya a kudancin Najeriya - NDLEA

Mun bankado kamfanin hada magunguna mafi hatsari a duniya a kudancin Najeriya - NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) ta ce ta gano wani kamfanin sarrafa magunguna inda aka gano kilogram 20 na kwayar Amphetamine a karamar hukumar Udi na jihar Enugu.

An bayyana cewa Amphetamine shafi kwaya mafi tsada da kuma hatsari a duk fadin duniya.

Kwamandan NDLEA na jihar, Dr. Anthony Nkem Ohanyere ne ya bayyana hakan a ranar duniya ra yaki da muggan kwayoyi na 2018 a hedkwatan hukumar da ke Enugu a jiya Laraba.

Mun bankado kamfanin hada magunguna mafi hatsari a duniya a kudancin Najeriya - NDLEA

Mun bankado kamfanin hada magunguna mafi hatsari a duniya a kudancin Najeriya - NDLEA

Kazalika, hukumar ta ce ta gano wani kamfanin magungunan a Umuokorouba a Ozalla da ke karamar hukumar Nkanu ta yamma inda nan ma ake sarrafa wasu muggan kwayoyi da aka haramta a Najeriya.

KU KARANTA: Abinda Buhari da Lalong suka fadawa jama'ar Filato

Ya kara da cewa hukumar ta kwato muggan kwayoyi misalin ton daya wanda ya yi dai-dai da 1000kg a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar.

Ohanyere ya ce irin gudunmawar da gwamnan jihar Ifeanyi Ugwuanyi ya ke bawa hukumar ne ya sa suka samu irin wannan gagarumin nasarorin.

An karrama gwamnan jihar ta hanyar saka sunansa a sabuwar dakin taro na hukumar da aka gama yiwa gyaran fuska a cikin kwanakin nan wadda gwamnan ya kaddamar.

A jawabinsa, Archnoshop na jihar Enugu, Most Reverend Dr. Emmanuel Chukwuma wanda shine babban taro a bukin ya yi kira ga mutane su bawa hukumar goyon baya don ganin an magance matsalar ta'amulli da miyagun kwayoyi.

A bamgarensa, gwamna Ugwuanyi ya sake jadada cewa ya kamata hukumar ta cigaba da ganin anyi biyaya ga dokoki tare da fadakar da al'umma da kuma bayar da taimako na magunguna da shawarwari ga masu son barin shan muggan kwayoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel