Dalilin da ya hana a cire Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Filato

Dalilin da ya hana a cire Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Filato

Sifeto Janar din 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya janye shirin sa na cire kwamishinan 'yan sandan jihar Filato, Undie Adie, domin bashi damar gabatar da bincike akan kashe kashen da ake yi a jihar

Dalilin da ya hana a cire Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Filato

Dalilin da ya hana a cire Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Filato

Sifeto Janar din 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya janye shirin sa na cire kwamishinan 'yan sandan jihar Filato, Undie Adie, domin bashi damar gabatar da bincike akan kashe kashen da ake yi a jihar.

Sama da rayuka 100 aka rasa tsakanin ranar 23 da 24 na watan yuni, a wasu Kauyuka na jihar Filato, sakamakon harin bata gari.

DUBA WANNAN: Zai yi shekaru 16 a gidan yari saboda ya bayyana ra'ayin sa a Facebook

An zabi Adie a matsayin kwamishinan yan sandan jihar a watan satumba, 2017,inda aka cire shi a ranar 26 ga watan yuni, inda ya koma kujerar shi a washegari.

Kamar yanda hukumar 'yan sandan ta sanar da manema labarai, an soke kawo sabon kwamishina, Bala Ciroma, domin a bawa Adie wanda yafi sanin yanda yankin, damar yin binciken da ya dace.

Sifeto Janar din ya tsige Adie ne sakamakon rashin hangen faruwar aika aikar, wanda yayi sanadin rasa rayuka da dama.

Majiyar mu tace, an yanke shawarar dawo da shi kujerar shi ne don yafi sanin yanayin yanda garin yake, domin hakan zai bashi damar yin binciken da ya dace.

Kashe kashen dai a jihar ba na kabilanci bane ko addini, kamar yanda wasu bangarorin suka bada rahoto.

Hukumar 'yan sandan tace, kashe kashen na siyasa ne, domin akwai wadanda aka tambaya jam'iyyar su kafin a kashe su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel