Gwamnoni sunyi taro akan karin albashi

Gwamnoni sunyi taro akan karin albashi

A ranar laraba da daddare ne kungiyar gwamnonin Najeriya suka hadu a Abuja, don tataunawa akan mafi karancin albashi, rashin tsaro da sauran matsalolin da ke kawo barazana ga cigaban kasar nan

Gwamnoni sunyi taro akan karin albashi
Gwamnoni sunyi taro akan karin albashi

A ranar laraba da daddare ne kungiyar gwamnonin Najeriya suka hadu a Abuja, don tataunawa akan mafi karancin albashi, rashin tsaro da sauran matsalolin da ke kawo barazana ga cigaban kasar nan.

A lokacin da kungiyar kwadago ke bukatar a maida Naira 65,000 a matsayin mafi karancin albashi, gwamnonin na assasa tabbatar da sabon albashin da wuri in an amince.

DUBA WANNAN: Kasashen musulmai guda 5 da zasu daina shiga kasar Amurka

A taron an tattauna akan matsalolin tsaro, musamman ma kashe kashen jihar Filato.

Gwamnonin zasu yi taro da shugaban Nigerian Postal service da kuma dukkanin manyan alkalai na jihohi 36 dake kasar nan.

Daga cikin abubuwan da zasu tattauna har da matsalolin zababbu da mahukuntan Gwamnatin.

Ana kuma bukatar matatar man fetur ta kasa da ta bayyana kudin shiga na mai da kuma kudin da matatar zata bada, wanda har yanzu shiru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel