Nigerian news All categories All tags
Sojin Najeriya sun yiwa 'Yan Boko Haram kwanton bauna, sun kwato Makamai da ceto Mutane 33 a Jihar Borno

Sojin Najeriya sun yiwa 'Yan Boko Haram kwanton bauna, sun kwato Makamai da ceto Mutane 33 a Jihar Borno

Mun samu rahoton cewa, hukumar sojin kasa ta Najeriya mai gudanar da aikin Operation LAFIYA DOLE, ta sake samun nasara kan 'yan ta'adda na Boko Haram cikin wasu kauyuka dake kananan hukumomin Bama da Damboa a jihar Borno.

Dakarun sojin dai kamar yadda rahotanni suka bayyana sun yiwa 'yan ta'addan kwanton bauna yayin da suke gudanar da wani sintiri na tsarkake duk wani lungu da sako na Arewa maso Gabashin kasar nan daga miyugun 'yan ta'adda na Boko haram.

Sojin Najeriya sun yiwa 'Yan Boko Haram kwanton bauna, sun kwato Makamai da ceto Mutane 33 a Jihar Borno

Sojin Najeriya sun yiwa 'Yan Boko Haram kwanton bauna, sun kwato Makamai da ceto Mutane 33 a Jihar Borno

Kamar yadda kakakin hukumar sojin ya bayyana a shafin ta na sada zumuntar facebook, Birgediya Janar Texas ya yi fashin baki dangane da yadda dakarun sojin suka kawar da wasu 'yan ta'adda shida daga doron kasa yayin bankade-bankade da sintiri a wasu sassa na jihar.

KARANTA KUMA: Wani dan Shekara 35 ya yiwa 'yar shekara 5 fyade a jihar Legas

A yayin da dakarun ke sauke nauyin da rataya a wuyan su cikin kauyukan Bulabuli, Falamari, Yerimari Gana da kuma Darel Salam, sun kuma samu nasarar kwato muggan makamai na kare dangi a hannun 'yan ta'addan kama daga bindigu zuwa bama-bamai da sauransu.

Legit.ng ta fahimci cewa, babbar nasarar dakarun sojin yayin wannan sintiri ita ce ceto mutane 33 daga hannun 'yan ta'addan da suka hadar da; Maza 8, Mata 12 da kananan yara 13 a ketaren yankunan karamar hukumar Bama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel