Nigerian news All categories All tags
Wani dan Shekara 35 ya yiwa 'yar shekara 5 fyade a jihar Legas

Wani dan Shekara 35 ya yiwa 'yar shekara 5 fyade a jihar Legas

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, wani Matashi dan shekaru 35 a duniya Achibong Koko, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda ta jihar Legas bisa laifin zakkewa wata karamar yarinya da shekarun ta ba su wuci biyar ba a duniya.

Rahoton dai ya bayyana cewa, Koko ya yiwa yarinyar fyade ne da misalin karfe 5.40 na yammacin ranar 24 ga watan Yuni a unguwar Dansa dake yankin Abule-Oshun na karamar hukumar Ojo a jihar ta Legas.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas; Imohimi Edgal

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas; Imohimi Edgal

Legit.ng ta fahimci cewa, Koko wanda ya kasance makwabcin Mahaifiyar wannan Yariyan ya samu nasarar aikata wannan aika-aikar ne yayin da ta kishingide wajen baccin rana.

KARANTA KUMA: Za'a fara Shari'ar Sufeto Janar na 'Yan sanda da Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Satumba

A yayin da wannan Mata ta farka daga barcin ta ne ta lura cewar diyar ta gaza tafiya daidai kamar yadda ta saba. Bayan bincikar ta ta kwashe labarin abin da ya faru da hakan yayi sanadiyar damkar Koko.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Imohimi Edgal, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari na ban takaici da ya bayyana cewa, an garzaya da ita asibiti inda Likitoci suka tabbatar da ta an tsallaka ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel