Nigerian news All categories All tags
PDP ta bawa mutanen jihar Filato shawarar abin da ya kamata su yiwa Buhari

PDP ta bawa mutanen jihar Filato shawarar abin da ya kamata su yiwa Buhari

- Kwamitin zartarwa na jam’iyyar na jam’iyyar PDP (NWC) ya shawarci jama’ar jihar Filato da su maka shugaba Buhari a kotun ICC

- Kazalika ta bayyana cewar, ta shiga alhini na tsawon kwanaki bakwai (7) domin jajantawa jama’ar jihar iftila’in da ya afka masu

- A jawabin da jam’iyyar ta fitar tab akin sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, PDP ta bukaci mutanen jihar Filato da hada kai

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar na jam’iyyar PDP (NWC) ya shawarci jama’ar jihar Filato da su maka shugaba Buhari a kotun shari’ar aikata laifukan aiyukan ta’addanci ta duniya (ICC) saboda kisan kare dangi da aka yi a jihar na baya-bayan nan.

Kazalika ta bayyana cewar, ta shiga alhini na tsawon kwanaki bakwai (7) domin jajantawa jama’ar jihar iftila’in da ya afka masu.

PDP ta bawa mutanen jihar Filato shawarar abin da ya kamata su yiwa Buhari

Ologbondiyan

A jawabin da jam’iyyar ta fitar tab akin sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, PDP ta bukaci mutanen jihar Filato da hada kai da wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama domin neman hakkin ‘yan uwan su da aka kashe da kuma asarar dukiya da suka yi sakamakon rigingimu, a karkashin gwamnatin Buhari.

DUBA WANNAN: Kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana su waye ke kashe mutane a Najeriya da sunan makiyaya

Duk ran dan Najeriya yana da muhimmanci, a saboda haka hakki ne a kan gwamnati ta kare rayukar dukkan jama’ar kasa ba tare da la’akari da kabilar su ko addini ko yankin da suka fito ba.

“Babba kuma muhimmin aiki da gwamnati zata yiwa jama’a shine kare rayukan su da dukiyoyin su. Haka tsarin yake ko ina a duniya, ba iya Najeriya ba kawai,” a cewar PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel