Nigerian news All categories All tags
Tsagwaron Kishin kasa: Zuciyar wani kwararren likitan Najeriya ta buga saboda cin da aka yiwa Najeriya jiya a Rasha

Tsagwaron Kishin kasa: Zuciyar wani kwararren likitan Najeriya ta buga saboda cin da aka yiwa Najeriya jiya a Rasha

Wani babban likita a bangaren kula da lafiyar iyali na asibitin koyarwa dake Abakaliki (FETHA) a jihar Ebonyi, Dakta Chidi Ebirim, ya fadi matacce a jiya, Talata, bayan Najeriya ta gaza samun nasarar zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake bugawa kasar Rasha.

Rahotanni sun bayyana cewar, Dakta Ebirim ya fadi ne bayan kasar Argentina ta zura wa Najeriya kwallo ta biyu a raga.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar an garzaya da kwararren likitan asibiti bayan ya fadi, amma duk da haka y ace ga garinku nan da safiyar yau, Laraba.

Tsagwaron Kishin kasa: Zuciyar wani kwararren likitan Najeriya ta buga saboda cin da aka yiwa Najeriya jiya a Rasha

Dan wasan da ya ci Najeriya kwallo ta biyu na murna

Yana kallon wasan kwallon ne a gidan sa. Amma sai kawai ya yanke jiki ya fadi bayan ya yi wata kara mai karfi yayin da aka saka wa Najeriya kwallo ta biyu a raga,” a cewar shaidar.

DUBA WANNAN: Kotun koli ta sahalewa Trump hana musulmi daga jerin kasashen nan shiga kasar Amurka

Mutuwar kwararren likitan ta jawo tsaiko a lamuran tiyata a asibitin, saboda dukkan likitocin dake aiki a asibitin sun shiga alhini da juyayin rtashin abokin aikin nasu.

Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) sun nuna matukar fushin su a kan wasan na jiya tare da zzargin yiwa kasar makarkashiya, ta hanyar hana ta bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kwallo ta taba hannun dan wasan baya na kasar Argentina a da'ira mai tsaron raga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel