Nigerian news All categories All tags
An maida Kwamishinan ‘Yan sandan Plateau kwana daya bayan cire shi

An maida Kwamishinan ‘Yan sandan Plateau kwana daya bayan cire shi

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa hukumar ’Yan sandan Najeriya, ta sanar da batun mayar da Undie Adie a matsayin sa na kwamishinan ’Yan sandan Jihar Plateau, kwana daya bayan maye gurbin sa da aka yi da Ciroma.

An yi wannan sanarwar ta mayar da Adie ne a yau Laraba, 27 ga watan Yuni kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Idan baza ku manta ba a jiya ne dai aka maye gurbin sa da Bala Ciroma, bayan ya shafe watanni tara kacal ya na kwamishinan ‘yan sanda a Plateau.

Shi ma kakakin ‘yan sanda na jihar, ya fitar da wata sanarwar da ke dauke da sake mayar da Adie da aka cire jiya.

KU KARANTA KUMA: Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda

Yayin da ake ta yada rudun cewa an tsige shi ne, ba cire shi aka yi da nufin maida shi wani wuri ba, sai kuma ga wata sanarwa cewa ya gaggauta komawa a kan mukamin sa a Plateau, ya gaggauta karbar iko daga hannun Bala Ciroma.

Jaridar Premium Times ta rahoto inda Adie ke cewa Sufeto Janar ne da kan sa ya yi tunanin sake maida shi a kan mukamin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel