Nigerian news All categories All tags
Hukumar NDLEA ta kama masu siyar da miyagun kwayoyi 290 a Kano

Hukumar NDLEA ta kama masu siyar da miyagun kwayoyi 290 a Kano

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta sanar da cewa a watanin shida da suka gabata, ta kama masu siyarwa da shigo da miyagun kwayoyi 290 a jihar.

Shugaban hukumar Hamza Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano a ranar Talata, 26 ga watan Yuni..

Umar ya bayyana cewa a cikin watanni shida hukumar ta gurfanar da wadanda ta kama da miyagun kwayoyin a babbar kotun jihar, sannan kuma ta kai mutane 117 asibiti a dalilin illar da shan kwayoyin ya yi musu.

Hukumar NDLEA ta kama masu siyar da miyagun kwayoyi 290 a Kano

Hukumar NDLEA ta kama masu siyar da miyagun kwayoyi 290 a Kano

“A takaice dai hukumar ta sami nasarar kama kwayoyin da suka kai giram 7,061.582 a cikin watanni shida da suka wuce.” Inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na shirin sake tsarin fasalin tsaron kasar - Dogara

Daga karshe ya yi kira ga sauran hukumomi masu farautar masu safarar miyagun kwayoyi da su taimaka musu domin ganin an kawo karshen haka a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel