Nigerian news All categories All tags
Wani jigo a PDP ya sauye sheka zuwa APC

Wani jigo a PDP ya sauye sheka zuwa APC

Mr Sunday Akinniyi, tsohon bulaliyar majalisar jihar Ekiti ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC kafin gabatar da zaben gwamna da za'ayi a jihar.

Akinniyi ya fice daga PDP ne a ranar Talata da ta gabata inda ya ce ya koma APC saboda rashin kulawa da hakkin mutane irin na gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti.

Ya zargin gwamna Fayose mai barin gado da rashin mutunta shugabanin jam'iyyar PDP.

Kamar yadda ya fadi "rashin kulawa da hakkin mutane" da Fayose keyi ya janyo rikice-rikicen cikin gida a jam'iyyar tare da ficewar mutane masu muhimmanci da yawa daga jam'iyyar ta PDP zuwa jam'iyyun adawa.

Wani jigo a PDP ya sauye sheka zuwa APC

Wani jigo a PDP ya sauye sheka zuwa APC

Tsohon dan majalisar da ke wakiltan Ikere II, ya fadi a sakatariyar yakin neman zaben Kayode Fayemi a Ado Ekiti cewa ya samu goyon bayan masu ruwa da tsaki a yankinsa kafin ya dauki matakin ficewa daga PDP.

KU KARANTA: Ina bukatar jike-jiken gargajiya - Nyame ya roki kotu daga gidan yari

Ya yi bayyanin cewa ya tsunduma cikin yakin neman zaben Dr. Fayemi ne saboda Fayose ya ci mutuncin basareke Olukere na Ikere bayan ya saba alkawarinsa na cewa sai karramashi tare da bashi sandan girma.

Ya kuma yi ikirarin cewa Fayose ya yi watsi da ayyuka masu muhimmanci a Ikere Ekiti.

"Gwamna Fayose ya nemi in gayyato masa Olukere kuma bayan na gayyato shi sai ya yi masa alkawarin cewa sai aika yan majalisar sarakuna su tafi fadan Olukere don ganin irin gyare-gyaren da ake bukata kuma zai kara wa kujerarsa daraja.

"Bayan an kai masa rahoton sai ya yi watsi da shi. Daga baya ma ya kula wa Olukere sharrin kisa kuma ya umurci jami'an tsaro su tsare shi, hakan yasa na goyi bayan dan takarar gwamna Farfesa Kolapo Olusola.

An tsige ni a matsayin bulaliyar jam'iyya ne saboda ina magana a kan rashin gudanar da ayyuka a mazaba ta ba wai don rashin aiki ko barci a yayin da ake zaman majalisa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel