Yanzu Yanzu: Buhari na shirin sake tsarin fasalin tsaron kasar - Dogara

Yanzu Yanzu: Buhari na shirin sake tsarin fasalin tsaron kasar - Dogara

Kakakin ajalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa shugabankasa Muhammadu Buhari na shirye-shiryen sake fasalin tsaron kasa domin magance matsalolin da yankunan kasar ke fuskanta.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuni a lokacin da ya zanta da manema labarai bayan ganawarsu da Buhari da Bukola Saraki.

Sai dai bai bayar da cikakken bayani akan batun sake fasalin lamuran tsaron ba.

Yanzu Yanzu: Buhari na shirin sake tsarin fasalin taron kasar - Dogara

Yanzu Yanzu: Buhari na shirin sake tsarin fasalin taron kasar - Dogara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu gungun yan bindiga dadi sun kashe dakarun rundunar Sojin kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da yan bindigar suka kai musu a cikin karamar hukumar Guma.

KU KARATA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya isa jihar Plateau

Majiyarmu ta ruwaito yan bindigan sun shirya wani tarko ne a daidai lokacin da Sojojin ke sintiri a a tsakanin kauyukan Umenger da Bakin korta, duk a cikin mazabar Mbadewem, a inda Sojoji biyu suka mutu, wasu kuma suka jikkata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel