Nigerian news All categories All tags
Yaki da rashawa: Tsohuwar Ministan Jonathan ta mayar da naira miliyan 640 cikin lalitar gwamnati

Yaki da rashawa: Tsohuwar Ministan Jonathan ta mayar da naira miliyan 640 cikin lalitar gwamnati

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da cewa wata tsohuwar Minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goolduck Jonathan ta maido da kudi naira miliyan dari shidda da arba’in (N640,000,000).

Legit.ng ta ruwaito Tsohuwar Ministan it ace Jumoke Akinjide, wanda ta rike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja na dan wan lokaci, amma sai ga shi t wawuri makudan kudade.

KU KARANTA: Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi

EFCC na tuhumar Akinjide ne, tare da shugaban PDP na jihar Oyo, Olarenwaju Otiti, tsohon Sanatan jihar Oyo Ayo Adeseun, da tsohuwar ministan albarkatun man fetir, Diezani Alison Madueke, wanda ta tsere daga Najeriya.

Yaki da rashawa: Tsohuwar Ministan Jonathan ta mayar da naira miliyan 640 cikin lalitar gwamnati

Minista

EFCC na tuhumarsu da satar kudi naira miliyan 650, inda tace naira miliyan 640 da ta maido baya cikin naira miliyan 650 da ake tuhumarsu da sacewa tare da Diezani, kamar yadda jami’in EFCC Usman Zakari ya bayyana, inda yace tun a shekarar 2016 ne Akinjide ta mika ma EFCC miliyan 10 daga cikin kudin da ta sata.

Usman Zakari, wanda shi ne shaidar EFCC a wannan shari’a da ake yi yace bayan miliyan 10 na farko da ta dawo da shi ga EFCC, wanda mijinta ya biya mata ta bankin Sterling, daga bisani ministan da kanta ta maido da cikon naira miliyan 640 ta bankin Stanbic IBTC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel