Nigerian news All categories All tags
Kofin duniya: Jami'an tsaro sunyi gargaɗi ayi hattara da harin ƴan ta'adda a gidajen kallon kwallo

Kofin duniya: Jami'an tsaro sunyi gargaɗi ayi hattara da harin ƴan ta'adda a gidajen kallon kwallo

- To fa masu zuwa gidan kallon kwallo sai ai hattara

- Domin hukumomin tsaro sunyi gargadin faruwar wani abu maras dadi

- Sun yi gargadin cewa watakila 'yan ta'adda ka iya amfanin da yanayin wajen kai hari

Hukumomi a Najeriya sun gargadi mutane da su zauna cikin shiri da kuma sa ido a yayin da suke kallon wasan kwallon kafar gasar cin kofin duniya, saboda akwai yiwuwar samun hare-hare a lokutan kallon wasanni.

Kofin duniya: Jami'an tsaro sunyi gargaɗi ayi hattara da harin ƴan ta'adda a gidajen kallon kwallo

Kofin duniya: Jami'an tsaro sunyi gargaɗi ayi hattara da harin ƴan ta'adda a gidajen kallon kwallo

Hukumar 'yan sanda tare da hukumar shige da fice ta kasa sun bayyana haka ne a ranar 25 ga watan Yulin da muke ciki, inda suka ce yan tada kayar baya suna nan suna kokarin ganin sun sake kawo farmaki wanda zai jefa jama'a cikin rudani, musamman a guraren da suke da cinkoson mutane domin kallon wasannin gasar cin kofin duniya.

Hukumar tsaro ta kasa ta bada umarni ga dukkanin wani shugaban yan sanda na kowace jiha da su kasance cikin shiri tare da tsaurara tsaro, sannan suke bada rahoton yanayin da kowace jiha take ciki lokaci zuwa lokaci.

KU KARANTA: Hanyoyi 5 da zaku bi don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa

Hukumar ta kara kira ga jami'an tsaro cewa ya kamata dukkan wani kayan tsaro su kasance cikin shiri domin komai zai iya faruwa, kuma tsaron dukiya da rayuwar al'umma ita ce abinda suka sa gaba.

Ya zuwa yanzu dai a iya cewa babu wata alama da aka gani game kallon wasanni da ake yi a gidajen kallo, kuma babu wani bayani da aka samu game da hakan, sai dai idan ba a manta ba a baya an samu gurare da dama wanda aka samu tashin boma-bomai.

A garin Damaturu a lokacin da ake wasan gasar cin kofin duniya a kasar Brazil a shekarar 2014, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Yuli 2014 tsakanin kasar Brazil da kasar Mexico inda bam ya tashi har mutane 21 suka rasa rayukansu sannan mutane 27 suka raunta.

Har wa yau, a shekara ta 2012 an samu inda wani bam ya tashi a gidan kallon kwallo a garin Jos dake jihar Plateau wanda shima mutane da dama suka raunata.

Najeriya dai ta tsinci kanta wajen yaki da yan tada kayar baya na Boko Haram tun shekara ta 2009 wanda hakan ya jawo salwantar rayukan mutane sama dubu goma (10,000) a yanki Arewa maso gabas kawai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel