Yanzu Yanzu: Saraki, Dogara na ganawar sirri da shugaban kasa Buhari

Yanzu Yanzu: Saraki, Dogara na ganawar sirri da shugaban kasa Buhari

Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara na cikin wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugabannin na ganawar ne akan kashe-kashe da aka yi a jihar Plateau a karshen makon da ya gabata.

Shugabannin majalisar dokokin Najeriya ne suka bukaci yin ganawar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu gungun yan bindiga dadi sun kashe dakarun rundunar Sojin kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da yan bindigar suka kai musu a cikin karamar hukumar Guma.

KU KARANTA KUMA: Wani kyakyawan matashi ya auri mata biyu a rana daya ya karfafawa sauran maza gwiwar yin haka

Majiyarmu ta ruwaito yan bindigan sun shirya wani tarko ne a daidai lokacin da Sojojin ke sintiri a a tsakanin kauyukan Umenger da Bakin korta, duk a cikin mazabar Mbadewem, a inda Sojoji biyu suka mutu, wasu kuma suka jikkata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel