Nigerian news All categories All tags
Buhari ya tursasa Obasanjo dawo da Kudaden Wutar Lantarki - Oshiomhole

Buhari ya tursasa Obasanjo dawo da Kudaden Wutar Lantarki - Oshiomhole

Sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ta matsa lamba akan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wajen dawo da makudan kudaden wutar lantarki.

Shugaban jam'iyyar ya nemi shugaba Buhari akan ya tabbatar da hujjar Tsohon shugaban kasa Obasanjo da ya yi ikirarin batar da Dalar Amurka Biliyan 16 wajen gyaran wutar lantarki yayin da yake mulkin kasar nan.

Legit.ng da sanadin shafin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, Oshiomhole ya nemi shugaba Buhari akan ya gurfanar da tsohon Shugaban kasa Obasanjo muddin ya gaza tabbatar da hujjar ikirarin sa ko kuma ya dawo da wannan kudade ga al'ummar Najeriya.

Buhari ya tursasa Obasanjo dawo da Kudaden Wutar Lantarki - Oshiomhole

Buhari ya tursasa Obasanjo dawo da Kudaden Wutar Lantarki - Oshiomhole

A ranar Talatar da ta gabata ne Oshiomhole ya bayyana hakan cikin jawaban sa a babban ofishin jam'iyyar APC dake garin Abuja yayin karbar mulki a hannun tsohon shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie-Oyegun.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun tsinto gawar wata Matar aure mai shekaru 20 a jihar Jigawa

Baya ga haka Oshiomhole ya jinjinawa tsohon shugaban jam'iyyar Odigie-Oyegun, sakamakon gudunmuwar sa da nasarori da jam'iyyar ta samu musamman a zaben 2015.

A nasa bangaren, Oyegun ya bayyana cewa yana da kyakkyawan zato kan kokari da jajircewa bisa aiki na Oshiomhole, inda yake sa ran nasarar jam'iyyar a zabuka masu gabatowa na jihar Osun da Ekiti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel