Gwamna Al-Makura ya kaddamar da kudirinsa neman kujerar majalisar dattawa

Gwamna Al-Makura ya kaddamar da kudirinsa neman kujerar majalisar dattawa

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa ya kaddamar da kudirinsa na neman kujerar dana majalisa na yankin Nasarawa ta Kudu a zaben 2019.

Gwamnan yace zai yi takarar ne a karkashin jam’iyyar All Progressive Congress, APC.

Ya bayyana hakan ne a sakatariyar APC na jihar dake Lafia a jiya Talata, 26 ga watan Yuni yayinda ya rantsar da sabbin jami’an jam’iyyar da aka zaba.

Gwamna Al-Makura ya kaddamar da kudirinsa neman kujerar majalisar dattawa

Gwamna Al-Makura ya kaddamar da kudirinsa neman kujerar majalisar dattawa

Gwamnan ya kuma karyata rade-radin cewa akwai wata sabani tsakaninsa da Sanata Abdullahi Adamu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki, Dogara na ganawar sirri da shugaban kasa Buhari

Ya kuma jaddada cewa shi babu wani dan takara da yake shirin tsayarwa a matsayin wanda zai gaje shi cewa shi babu wanda zai dauki nauyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel