Nigerian news All categories All tags
Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Mista Sunday, tsohon bulaliyar majalisar dokoki na jihar Ekiti, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC gabannin zaben gwamna wanda za’a yi a ranar 14 ga watan Yuli.

Akinniyi ya sauya sheka a ranar Talata, 26 ga watan Yuni inda ya bayyana dalilinsa da cewaya koma APC ne saboda rashin azancin Ayodele Fayose.

Ya zargi gwamnan da rashin girmama manyan shugabannin jam’iyyar PDP.

Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Wani babban jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Ya bayyana cewa hakan ya janyo rikici da yawan sauya sheka na manyan masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe Rahma Indimi ta yi magana akan baikon kanwarta

Ya kuma yi zargin cewa Fayose yayi watsi da mazabarsa da kuma manyan aikin yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel