Nigerian news All categories All tags
Namu ya samu: Matasan jihar Kaduna su 3000 zasu sharɓi romon Dimukradiyya a gwamnatin Buhari

Namu ya samu: Matasan jihar Kaduna su 3000 zasu sharɓi romon Dimukradiyya a gwamnatin Buhari

Babban bankin Najeriya, CBN, ta kammala tantance matasa guda dubu uku da suka fito daga jihar Kaduna wanda zasu samu amfana da shirin noma da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kirkiro, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin jihar Kaduna ce ta sanar da haka ta bakin Kaakakin ma’aikatar noma da gandun daji na jihar Yusuf Abdullahi ya bayyana, inda yace tsarin zai tallafa ma matasa akan al’muran noma don habbaka tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Tsokalo tsuliyar Dodo: Yan bindiga sun hallaka Dakarun Sojoji guda 2

“Matasa dubu bakwai, 7000, ne suka mika bukatar cin gajiyar wannan shiri, zuwa yanzu mun samu sunayen mutane dubu uku daga cikinsu, wadanda CBN ta kammala tantance, kuma nan bada jimawa ba zasu fara samun kayan aikin noma na naira dubu Talatin hudu, N34,000 a duk Eka daya na gona.” Inji shi.

Majiyar ta ruwaito wannan tsari na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya a kokarin samar da isashshen abinci a kasar gaba daya, da kuma damar diban matasa dubu goma aiki a kowanni jihar.

Rawar da gwamnatocin jihohi zasu taka ya hada da samar da filayen noma, gina titi zuwa gonakan, tare da horas da matasan kan dabarun noma, yayin da gwamnatin tarayya zata samar da kudaden aiki ga matasan.

Jihar Kaduna ta zabi kiwon kaji, noman shinkafa da kuma noman alkama, sune irin noman da ake sa ran matasan daga suka fito daga jihar Kaduna su 3000 zasu karkata, inda ake sa ran zasu samar da buhuna goma sha biyar, tare da biyan bashin da aka basu aka basu da buhu uku.

Haka zalika an raba takardar nema shiga ga Mata da matasa dubu goma, na wani sabon tsarin tallafa ma yan Najeriya wanda gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin gwiwar yan Kaduna mazauna kasar Birtaniya suka kirkiro, wanda a yanzu haka manoma dubu biyu na cin gajiyarsa a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel