Nigerian news All categories All tags
Ni kadai nake wahala: Wani gwamnan jihar Arewa ya koka, ya ce mutanen day a nada basa tabuka komai

Ni kadai nake wahala: Wani gwamnan jihar Arewa ya koka, ya ce mutanen day a nada basa tabuka komai

- Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, y ace mutanen day a nada a mukamai basa tabuka komai

- Ya ce masu rike da mukaman siyasar basa kare shi ko gwamnatin sa

- Gwamnan ya bukaci sabbin mutanen day a nada da su zage dantse domin kawo canji

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya koka a kan yadda mutanen da ya nada a mukaman siyasa suka guje shi.

Gwamnan na wadannan kalamai ne ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Benuwe dake Makurdi yayin rantsar da wasu sabbin nade-nade da ya yi, kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito.

Ni kadai nake wahala: Wani gwamnan jihar Arewa ya koka, ya ce mutanen day a nada basa tabuka komai

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Gwamnan ya koka a kan yadda masu rike da mukaman siyasa da ya nada basa iya kare shi ko gwamnatin sa yayin da ‘yan adawa ke caccakar sa ko salon mulkin sa. Ya kara da cewa, “maimakon su kare ni ko gwamnati na sai kawai su yi shiru.

Kazalika, ya yi kaimi ga sabbin wadanda ya nada das u zage dantse domin tabbatar da nasarar gwamnatin sa a kowanne mataki.

DUBA WANNAN: Kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana su waye ke kashe mutane a Najeriya da sunan makiyaya

Ni nasan cewa ba ni da abokan tafiya a cikin gwamnati. Ni kadai nake shan wahala. Na basu dama ga mutanen da basu cancanta ba, mutanen da basa kishi na ko na gwamnati na domin tamkar ni kadai nake tafiyar da al’amuran gwamnati,” a cewar Ortom.

Kazalika, Ortom ya karyata maganar dake yawo a gari na cewar shine ya aike da takardar korafi ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) hart a kai ga sun kama tsohon gwamnan jihar, Gabriel Suswan, tare da bayyana cewar bashi da hannu a cikin halin da tsohon gwamnan ke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel