Nigerian news All categories All tags
Tashar ruwan kan tudun da ke Kaduna ta kawowa Najeriya Biliyoyi cikin wata 6

Tashar ruwan kan tudun da ke Kaduna ta kawowa Najeriya Biliyoyi cikin wata 6

- Tashar ruwan da ke kan tudu a Arewcin Najeriya ta fara kawo kudin shiga

- Najeriya ta samu Biliyan 2 wajen hada-hadar kaya a tashar a shekarar nan

- A farkon shekarar nan ne Shugaban Kasa Buhari ya bude tashar a Kaduna

A makon nan ne mu ka samu labari cewa tashar bisar da aka kaddamar farkon shekarar nan a Jihar Kaduna ta jawowa Najeriya makudan kudin da su ka haura sama da Naira Biliyan 2.

Tashar ruwan kan tudun da ke Kaduna ta kawowa Najeriya Biliyoyi cikin wata 6

Tashar ruwan kan tudun Kaduna ta fara kawo kudin shiga

Shugaban Hukumar tashar ruwa ta kan kudun da ke Kaduna KIDP Tope Borisade ya bayanawa ‘Yan jarida a Legas cewa daga lokacin da aka bude tashar a Watan Junairun nan zuwa yanzu an samu kudi har Naira Biliyan 2.

KU KARANTA: An saki Sanata Abaribe bayan yayi makonni a tsare

Mista Borisade ya kuma bayyana cewa Hukumar kwastam tayi wa tashar lasisin daukar kaya. Bugu da kari ma dai yanzu babban bankin Najeriya CBN sun san da zaman tashar ta kan tudu wanda ita ce ta farko a Yankin.

A wancan lokaci kun ji cewa tashar ta kan tudu za ta taimaka wa 'yan kasuwar da ke Yankin Arewa wajen rage wahalhalun zuwa Kudu domin karbar kayansu ko fitar da su zuwa waje ba tare da kashe kudin sufuri ta ruwa ba.

A bana ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bude tashar ruwa da ke kan tudu ta farko a Najeriya . Wannan tasha ta na taimakawa 'yan kasuwar da ke Arewa da ke nesa da teku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel