Kashe-Kashen Jihar Filato: Sufeto Janar ya tsige Kwamishinan 'Yan sanda

Kashe-Kashen Jihar Filato: Sufeto Janar ya tsige Kwamishinan 'Yan sanda

Bayan kimanin tsawon sa'o'i 48 da kisan sama da mutane 100 a kananan hukumomin Barkin Ladi, Riyom, da Jos ta kudu a jihar Filato, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin tsige kwamishinan 'yan sanda na jihar, Undie Adie kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda Bala Ciroma dan asalin jihar Yobe, shine zai maye gurbin wannan kujera a jihar ta Filato.

Wani takaitaccen rahoto na ranar Talatar da ta gabata da sanadin kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Matthias Tyopev ya bayyana cewa ba bu wani dalili dangane da tumbuke kwamishinan na 'yan sanda daga mukamin sa.

KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa wasu Dillalai 5 na Muggan 'Kwayoyi hukuncin Kisa

Legit.ng ta fahimci cewa, a shekarar 1988 ne Kwamishina Ciroma ya kammala karatun digiri na farko a jami'ar Maiduguri, inda ya shiga makarantar koyan aikin 'yan sanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990.

Ya rike makumai daban-daban yayin gumurzu bisa aiki cikin kusan duk rassa shida na kasar nan tare da rike babban mukami a hukumar han yiwa tattalin arziki zagon kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel