Nigerian news All categories All tags
Gwamna Ganduje ya samu kyauta a matsayin Gwamnan da ya fi kowa yaki da shan kwayoyi

Gwamna Ganduje ya samu kyauta a matsayin Gwamnan da ya fi kowa yaki da shan kwayoyi

Labari ya zo mana cewa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu jinjina daga Hukumar yaki da rashin gaskiya da mugayen kwayoyi watau ARDI. Hukumar tace Gwamnan ne kan gaba wajen yaki da barna a Najeriya.

Gwamna Ganduje ya samu kyauta a matsayin Gwamnan da ya fi kowa yaki da shan kwayoyi

Gwamnan Jihar Kano Ganduje ya karbi lambar yabo

Hukumar ta ARDI ta bayyana Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Gwarzo wajen yaki da rashin gaskiya ta dakile harkar miyagun kwayoyi. Shugaban Hukumar na ARDI Cif Dennis Aghanya ne ya ba sa wannan kyautar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bude wani katafaren asibiti a Najeriya

Gwamnan na Kano yayi kokari wajen kafa Hukumomin yaki da cin hanci a kowace karamar Hukuma na Jihar Kano. Hakan dai yasa an samu gaskiya da tsabta a yadda ake gudanar da ayyuka a Jihar ta Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Yanzu dai Jihar ta Kano ta na cikin Jihohin da ke koyi da muradun Shugaba Buhari na yaki da rashin gaskiya. Gwamna Ganduje ya samu wannan nasara ne ta hanyar maganin shaye-shaye da Matasa ke yi a Jihar cikin shekaru 3 da yayi a mulki Inji ARDI.

Shugaban Hukumar karbar korafi da kuma yaki da rashin gaskiya a Jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya wakilci Gwamnan a wajen karbar wannan kyauta da Hukumar ta ARDI mai yaki da rashin gaskiya da amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel