Nigerian news All categories All tags
Kotun koli ta sahalewa Trump hana musulmi daga jerin kasashen nan shiga kasar Amurka

Kotun koli ta sahalewa Trump hana musulmi daga jerin kasashen nan shiga kasar Amurka

Kotun koli a kasar Amurka ta amince da kudurin shugaban kasar na hana mutane daga wasu kasashen musulmi shiga kasar.

Kananan kotuna a kasar Amurka sun yi watsi da bukatar shugaba Trum na haramtawa musulmi daga kasashen shiga kasar, su na masu bayyana cewar yin hakan ya sabawa tsarin mulki da dokokin kasar.

Amincewar kotun kolin ga wannan doka zai shafi musulmi daga kasashen Iran, Libya, Somalia, Yemen da Siriya.

Kotun koli ta sahalewa Trump hana musulmi daga jerin kasashen nan shiga kasar Amurka

Trump da Sarki Salman na Saudiyya

Duk da kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na ‘yan gudun hijira sun yi ala-wadai da wannan doka, ana kallon hukuncin kotun a matsayin wata gagarumar nasara ga gwamnatin shugaba Trump.

Da yake bayyana amincewa da dokar, Babban alkali John Roberts, y ace ikon shugabanci ya bawa shugaban kasa dammar daukan irin wannan mataki musamman idan akwai barazanar tsaro.

DUBA WANNA: Kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana su waye ke kashe mutane a Najeriya da sunan makiyaya

Saidai wani darakta a wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta ACLU dake kasar ta Amurka ya bayyana hukuncin da cewar gazawa c eta kotun.

Tun kafin hawan sa mulki shugaba Trump ya dauki alkawarin hana mutane daga wasu kasashen musulmi shiga kasar ta Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel