Nigerian news All categories All tags
Yanzu - Yanzu: DSS ta saki Sanata Abaribe bayan tsare shi na kwanaki hudu

Yanzu - Yanzu: DSS ta saki Sanata Abaribe bayan tsare shi na kwanaki hudu

Rahottani da muka samu a yanzu na nuna cewa hukumar tsaro na farar hula DSS ta sake Sanata Enyinnaya Abaribe bayan tsare shi na kwanaki hudu.

Kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito, lauyansa da masu taimaka masa suna hedkwatan hukumar DSS da ke Abuja inda suke cike takardun sakin sa.

An dai kama Sanata Abaribe ne a ranar Juma'a kuma aka tsare shi a wani boyayen wuri saboda wasu dalilai da ba'a bayyana ba, ana kyautata zaton kamun da a kayi masa ba zai rasa nasaba da dangartakarsa da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Yanzu - Yanzu: DSS ta saki Sanata Abaribe bayan tsare shi na kwanaki hudu

Yanzu - Yanzu: DSS ta saki Sanata Abaribe bayan tsare shi na kwanaki hudu

KU KARANTA: Wani babban basarke a Zamfara ya bayyana silar kashe-kashen mutane a jihar

A safiyar yau Talata, an gurfanar da Abaribe a gaban Justice Binta Murtala-Nyako don ya kare kansa a matsayinsa na wanda tsayawa Nnamdi Kanu jingina kafin a bayar da belinsa kuma yanzu ya tsere tun watan Satumban 2017.

Hukumar DSS ne ta kai Abaribe kotu kuma bayan ya amsa tambayoyin da a kayi masa sai suka mayar dashi hedkwatan hukumar.

Yan kungiyar IPOB sunyi tururuwa zuwa kotun don nuna goyon bayansu ga Sanata Abaribe inda har suka rike takardu dauke da rubutu na cewa kotun ta saki Abaribe.

Jim kadan bayan kammala sauraran karar nasa a kotu ne DSS suka yiwa lauyoyinsa waya inda suke umurcesu da su zo su sanya hannu a kan takurdun sakinsa.

A lokacin rubuta wannan rahoton, lauyoyin Abaribe, Chukwuma Uche (SAN) da Aloy Ejimakor da Ifeanyi Iboko tare da wadanda za su tsaya masa jingina sun isa ofishin DSS inda za su karbe shi bayan cike takardun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel