Nigerian news All categories All tags
Kotu ta yankewa wasu Dillalai 5 na Muggan 'Kwayoyi hukuncin Kisa

Kotu ta yankewa wasu Dillalai 5 na Muggan 'Kwayoyi hukuncin Kisa

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, a ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar Kotun tarayya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu Mutane biyar bisa laifin dillancin muggan kwayoyi a yankin Shanxi na Arewacin Kasar Sin.

Hakazalika Kotun ta zartar da hukuncin kisa kan wasu Mutane shida bisa laifin fataucin muggan kwayoyi inda suke da damar shekaru biyu na kotun cikin tanadin ta na shari'a ta sauya wannan hukunci.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Kotun ta kammala binciken ta kan wasu Mutane 32 da suka aikata laifukan da suka shafi fataucin muggan kwayoyi cikin kasar ta Sin.

Kotu ta yankewa wasu Dillalai 5 na Muggan 'Kwayoyi hukuncin Kisa

Kotu ta yankewa wasu Dillalai 5 na Muggan 'Kwayoyi hukuncin Kisa
Source: UGC

Kotun ta zartar da hukuncin zama gidan kaso na dindindin kan wasu Mutane 14 tare da hukuncin zama a gidan kaso kan wasu mutane bakwai na wa'adin da bai wuci kasa da shekaru biyu ba.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da aikin hanya daga Kano zuwa Abuja

Hakazalika kotun ta gurfanar da wasu Mutane 25 da suka aikata laifi na fataucin muggan kwayoyi cikin kasar a tsakanin watan Agusta na shekarar 2015 da watan Maris na shekarar 2016.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yau ne Talata 26 ga watan Yuni tayi daidai da ranar tunawa da yaki da fataucin muggan kwayoyi ta duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel