Nigerian news All categories All tags
Kasashe da aka haramta amfani da Niqabi

Kasashe da aka haramta amfani da Niqabi

Duk da ikirarin kare hakkin dan Adam da sukeyi, kasashen Turai da dama sun hana Musulmai bin umurnin addininsu na sanya Niqabi. A kasashe da dama an haramta sanya Niqabi, Legit.ng ta kawo muku kasashe goma da suka hana sanyawa.

1. Kasar Faransa

Kasar Faransa ce kasar Turai ta farko da ta haramtawa sanya Niqabi a bainar jama’a. Wannan doka ya fara aiki a shekarar 2004. A shekarar 2011, shugaban kasar Nicolas Sarkozy y ace basu son Niqabi a kasar su.

2. Belgium

Belgium ta biyo sahun Faransa ne a shekarar 2011 kuma ta sanya taran Yuro 1378 da garkaman kwanaki 7 a kurkuku ga duk wacce aka kama sanye da Niqabi  

3. Kasar Holland

A shekarar 2015, kasar Netherland ta haramta sanya Niqabi a makarantu, asibiitoci da kuma abubuwan hawa na haya. Su basu haramta gaba daya ba amma sai a wadannan wurare.

4. Kasar Italia

Kasar Italy bata haramta a fadin kasar gaba daya ba amma a wasu jihohin kasar, sun haramta musamman a wajajen shakatawa.

5. Kasar Spain

Wasu sassan Catalonia a kasar Spain sun haramta Niqabi. A shekarar 2013, kotun kolin kasar tayi watsi da dokan saboda hakan taka hakkin mabiya addini ne.

6. Kasar Chadi

An hana mata amfani da Niqabi a kasar Chadi tun harin kunar bakin waken da aka kai har sau biyu a shekarar 2015.

7. Kamaru

Kasar Kamar ta biyo sahun kasar Chadi amma a jihohi 5 kawai wannan ke da karfi a kasar

8. Nijar

An haramta amfani da Niqabi a Diffa, kasar Nijar bisa ga hare-haren Boko Haram.

9. Congo-Brazzaville

10. Switzerland

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel