Nigerian news All categories All tags
Gasar cin kofin Duniya: Magen sa’a ta bayyana Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina

Gasar cin kofin Duniya: Magen sa’a ta bayyana Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina

Wata kyanwa mai suna Achilles ta sanar da cewa Najeriya za ta lallasa kasar Ajantina a wasan da kasashen biyu zasu fafata a daren Talata, 26 ga watan Yuni da misalin karfe 7 na yamma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai wani abin mamakai shine wannan Mage ta bayyana wadanda zasu yi nasara a dukkanin wasanni guda uku da aka buga su a babban birnin kasar Rasha, St Petersburg, kuma dukkanin wanda ta zaba zai ci, shi ya samu nasara akan abokin karawarsa.

KU KARANTA: Dalibai sun debo ruwan dafa kansu: Jami’ar Jihar Kano ta ci tarar kowanne dalibi N13,000

Wasanni uku da Achilles da has ashen Achilles yayi daidai suna cewa Iran zata lallasa Morocco, Russia za ta lallasa kasar Masar, da kuma cewa Brazil za ta samu nasara akan kasar Costa Rica, toh yanzu idan hasashen Achilles ya tabbata, Najeriya zata haura zuwa zagaye na gaba kenan.

Gasar cin kofin Duniya: Magen sa’a ta bayyana Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina

Kyanwa Achilles

Ita dai Achilles wanda ake tsaronta a gidan ajiyan kayan tarihi na Hermitage, ta zabi kasar Najeriya ne bayan da aka ajiyeta a gaban masu daukar hoto, sa’annan aka ajiye mata kwanukan guda biyu, da aka jingina tutar Najeriya a daya, guda kuma tutar Ajantina.

Jim kadan bayan ta kwashe wani dan lokaci tana tunani, sai kwatsam ta hau kwanun dake dauke da Najeriya tana cin abincin dake cikinsa da sauri sauri, wanda hakan ke alanta Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina.

Wannan wasa shine na karshe a rukunin D, wanda zai baiwa duk wanda ya samu nasara a tsakanin Najeriya da Ajantina damar hayewa zagaye na gaba, inda dayan kuma zai koma gida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel