Nigerian news All categories All tags
Rikicin makiyaya da manoma: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Jos (Hotuna)

Rikicin makiyaya da manoma: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Jos (Hotuna)

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Jos na jihar Filato, bayan saukarsa a filin sauka da tashin jirage na Yakubu Gowon, dake unguwar Heipang a cikin karamar hukumar Barikin Ladi na jihar, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya isa garin ne don gane ma kansa barnar da rikicin makiyaya da manoma ya haifar tare da jajanta ma al’ummar jihar, musamman wadanda matsalar ta shafa.

KU KARANTA: Dalibai sun debo ruwan dafa kansu: Jami’ar Jihar Kano ta ci tarar kowanne dalibi N13,000

Rikicin makiyaya da manoma: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Jos (Hotuna)

Buhari a Jos

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, mataimakinsa Sonnie Tyoden, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Pauline Tallen, sabon kwamishinan Yansandan jihar da sauran shuwagabannin hukumomin tsaro ne suka tarbi Buhari yayin da ya sauka a filin jirgin.

Wani sabon rikicin kabilanci tsakanin makiyaya da manome dai ya barke a karshen makon da ta gabata, inda akalla mutane dari suka rasa rayukansu, baya ga tarin dukiya da aka tafka asara.

Ana sa ran Buhari zai yi wata tattaunawa da shuwagabannin hukumomin tsaro, manyan jami’an gwmanatin jihar da ma sauran masu ruwa da tsaki na jihar, don lalubo bakin zaren tare da shawo kan rikice rikicen.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, sai da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar ba zata jihar Filato duk akan wannan rikici na makiyaya da manoma, inda ya zazzagaya yankunan jihar inda rikicin ya shafa, tare da tattaunawa da gwamnan jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel