Nigerian news All categories All tags
Hukumar 'Yan sanda ta cafke wata Mata da laifin cin zarafi a Garin Abuja

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wata Mata da laifin cin zarafi a Garin Abuja

Wani rahoto da shafin jaridar The Nation ta ruwaito ya bayyana cewa, hukumar 'yan sanda ta cafke wata Mata mai shekaru 27 Joy Orji, tare da gurfanar da ita a gaban kotun Karmo dake babban birnin Kasar nan Abuja bisa laifin Cin zarafi.

Wannan Mata Orji wadda mazauniyar unguwar Idu daura da 'yan Katako a gundumar Karmo ta Abuja ta shiga hannun jami'ai ne da laifin cin zarafi da ya wuce gona da iri da ya sabawa sashen nan 265 na dokar Kasa.

Misis Okagha Ijeoma, jami'ar 'yan sanda mai shigar da kara a gaban kotu ta bayar da shaidar cewa, wata Mata Goodness Obi ita tayi karar Orji a ofishin su na 'yan sanda tun a ranar 17 ga watan Yuni.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wata Mata da laifin cin zarafi a Garin Abuja

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wata Mata da laifin cin zarafi a Garin Abuja

Legit.ng ta fahimci cewa, korafin Obi akan Orji bai wuci bankadowa cikin gidan ta ba yayin da take sulala sanwa inda ta ci mata mutunci tare da nuna ta da manuniyar yatsa ba tare da wani dalili ba.

KARANTA KUMA: Kujerar Shugaban Kasa: Makarfi ya samu goyon bayan Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna a Zaben 2019

Hakazalika korafin Obi kamar yadda ta bayar da shaida ya bayyana cewa, Orji ta kiraye da sunayen banza na cin fuska gami da aibatawa tare da kiran ta wulakantattar Mace.

Baya ga haka kuma Orji ta yi barazanar maganin Obi tare da cewar wahala ba ta kare mata ba a rayuwa domin kuwa haka za ta dawwama har mutuwar ta.

Sai dai yayin gudanar da Shari'ar, Alkalin kotun Mista Maiwada Inuwa ya bayar da belin Orji kan kudi Naira dubu Ashirin tare da daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Agusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel