Nigerian news All categories All tags
Babbar Magana: Hukumar kwastan zata fara sintiri a jiragen yakin domin farautar masu sumogal

Babbar Magana: Hukumar kwastan zata fara sintiri a jiragen yakin domin farautar masu sumogal

A kokarin ta na cigaba da yaki da masu safarar haramtattun kaya zuwa Najeriya, hukumar hana fasa kwabri da aka fi sani da kwastam ta bayyana cewar ta fara tunanin mallakar jiragen yaki da ragowar wasu na’urori masu sarrafa kan su domin yakar ‘yan sumogal masu kunnen kashi.

Mataimakin shugaban hukumar kwastam na kasa, Aminu Dangaladima, ne ya sanar da haka ga manema labarai a jiya, Litinin, yayin da yake kaddamar da wasu Karin motocin sintiri guda 30.

Babbar Magana: Hukumar kwastan zata fara sintiri a jiragen yakin domin farautar masu sumogal

Jirgin yaki

Da yake amsar tambaya a kan yiwuwar amfani da kimiyyar zamani domin kawo karshen safarar haramtattun kayayyaki zuwa Najeriya, Dangaladima ya bayyana cewa, “muna tunanin fara amfani da jiragen yaki. Zamu hada kai da hukumar sojin sama, sannan muna tunanin amfani da wasu na’urori masu sarrafa kan su. Muna kan hanyar cimma hakan da yardar Allah.”

DUBA WANNAN: Tsohuwar minista ta amayar da miliyoyin kudin makamai da ta hadiya bayan ta ji matsar EFCC

Sannan ya kara da cewa yaki da masu safara ban a hukumar kwastam ba ne kadai tare da bayysns cewar dole su hada kai da ragowar hukumomin tsaro.

Kazalika ya yi kira ga al’ummar da garuruwan su ke kan iyakokin Najeriya da suke taimakawa hukumar ta kwastam ta muhimman bayanai a kan masu safara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel