Nigerian news All categories All tags
Dalibai sun debo ruwan dafa kansu: Jami’ar Jihar Kano ta ci tarar kowanne dalibi N13,000

Dalibai sun debo ruwan dafa kansu: Jami’ar Jihar Kano ta ci tarar kowanne dalibi N13,000

Mahukunta jami’ar kimiyya na jihar Kano dake garin Wudil ta sanar da rusa gwamnatin dalibai na jami’ar tare da cin su tarar kudi naira dubu goma sha uku, N13,000 akan kowane dalibi sakamakon barnar da daliban suka tafka a yayin wata zanga zanga da suka gudanar.

Jaridar The Nation ta ruwaito shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji Musa ne ya sanar da haka a ranar Talata, 26 ga watan Yuni, inda yace daliban sun tafka wannan barna ne a yayin wata zanga zanga da suka yi a ranar 2 ga watan Mayu.

KU KARANTA: bWata sabuwa: Kalli wasu shanu dake kiwo a cikin majalisun dokokin Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesan yana cewa barnar da daliban suka tafka ta kai ta naira miliyan dari biyar, (500,000,000), a sanadin nuna bacin ransu da mutuwar wani dalibi da ya shiga ruwan wudil don yin wanka.

Dalibai sun debo ruwan dafa kansu: Jami’ar Jihar Kano ta ci tarar kowanne dalibi N13,000

Jami'ar

Farfesan yace akalla a wurare 21 daliban suka tafka barna iri iri, tare da farfasa abubuwa sama da guda 100, daga ciki har da wata motar daukan marasa lafiya da darajarsa ta kai naira miliyan Arba’in, cibiyar kimiyya da fasaha inda aka lalata na’urori na miliyan 250, asibitocin makarantar, motoci.

Sauran sun hada da Ofishin jami’an tsaron makarantar, dakunan kwanan Mata da Maza, dakunan gwaje gwaje, Azuzuwan karatu, na’urorin cire kudi guda biyu na bankin Zenith, tsangayar karatu, da duk wasu manyan allunan talla da na bayanai.

“Don haka bayan tattaunawa, majalisar koli ta jami’ar a zamanta na 84 ta amince da bude jami’ar a ranar 9 ga watan Yulin shekarar 2008, haka zalika an ci tarar kowane dalibi N13,000 da kudin gwajin lafiya N4,000. Daga karshe kwamitin ta rusa gwamnatin dalibai nan da take.” Inji shi.

Daga karshe Farfesa Musa yace babban jami’I mai kula da al’amuran dalibai zai karbi ragamar tafiyar da ayyukan gwamnatin daliban, sa’annan yace za’a kafa wata kwamitin wakilan dalibai da ake sa ran tabbatar da cigaban daliban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel