Nigerian news All categories All tags
Jami'an tsaro sun ci mutunci tsohuwar minista a kofar fadar shugaban Kasa, kalli hotuna

Jami'an tsaro sun ci mutunci tsohuwar minista a kofar fadar shugaban Kasa, kalli hotuna

Wasu jami'an tsaro da ke aiki a fadar shugaban kasa wato Aso Rock sun ci mutuncin tsohuwar ministan ilimi Oby Ezekwesili yayin da tafi fadar shugaban kasar don yin zanga-zanga a ranar Talata.

An dai fara zanga-zangar ne a sakatariyar gwamnatin tarayya amma aka tarwatsa mastu zanga-zangar yayin da suka iso gaban fadar shugaban kasa.

Jami'an tsaron da suke gadi a kofar shiga Aso Rock sun yi amfani da karfi wajen kwace kwalin da ta ke rike dashi.

Tsohuwar ministan ta ki bari jami'an tsaron su kwace kwalin ta yadda wanda hakan ya janyo ya bangaje ta.

Jami'an tsaro sun cakusa tsohuwar ministan Jonathan a kofar shiga Aso Rock

Jami'an tsaro sun cakusa tsohuwar ministan Jonathan a kofar shiga Aso Rock

An kuma kwace wayoyi da Kyamaran daukan hotuna daga hannun yan jarida da ke nade abubuwan da ke wakana a wajen.

Jami'an tsaro sun cakusa tsohuwar ministan Jonathan a kofar shiga Aso Rock

Jami'an tsaro sun cakusa tsohuwar ministan Jonathan a kofar shiga Aso Rock

A baya dai, Ezekwesili ta shaidawa manema labarai cewa bata gamsu da irin tafiyar hawainiyar da shugaba Buhari ya keyi wajen magance matsalolin tsaro da ke adabar kasar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel