Nigerian news All categories All tags
Buhari ya ba da umurnin sauya jami’an yan sanda a jihar Zamfara saboda tabbatar da tsaro

Buhari ya ba da umurnin sauya jami’an yan sanda a jihar Zamfara saboda tabbatar da tsaro

Rahotanni sun kawo cewa a kokari da ake na ganin an wanzar da zaman lafiya a jihar Zamfara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin chanja yan sandan jihar Zamfara.

A cewarsa hakan zai tabbatar da dakile ayyukan ta’addanci da barayin shanu ke aiwatarwa a jihar.

Buhari ya fadi hakan ne jiya a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja yayin da yake ganawa da tawagar kungiyar shari’a wato 'Supreme Council for Sharia in Nigeria'.

Buhari ya ba da umurnin sauya jami’an yan sanda a jihar Zamfara saboda tabbatar da tsaro

Buhari ya ba da umurnin sauya jami’an yan sanda a jihar Zamfara saboda tabbatar da tsaro

Shugaban ya kara da cewar, yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya shawo kan matsalolin tsaron jihar Zamfara da sauran sassan kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Atiku: DSS sun hana yan jarida daga shiga filin jirgin Asaba

Buhari ya cigaba da cewar, sakamakon rashin gamsuwa da kokarin jami'an yan sanda a jihar Zamfara, ya yi umurnin sauya manyan jami'an yan sanda na jihar da kuma kananan yan sandan da suka kai shekaru uku suna aiki a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel