Nigerian news All categories All tags
Ina farin ciki na hana kaina da ma’aikatana amfana da kwangila - Buhari

Ina farin ciki na hana kaina da ma’aikatana amfana da kwangila - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai taba shiga kurkuku ba saboda ya gamsu da abinda Allah ya bashi.

A wani jawabi da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya saki, shugaba Buhari ya bayyana cewa bai dogara da kwangila daga ayyulan gwamnati.

“Na shiga wurare da dama har da (ma’aikatar) man farue. Da na shiga kurkuku da na dau rijiyan mai daya. Ban nadamar rike gaskiya da amana.”

“Na godewa Allah da abinda ya bani. Na yi farin cikin hana kaina da makusantana amfana da kwangilolin gwamnati.”

Ina farin ciki na hana kaina da ma’aikatana amfana da kwangila - Buhari

Ina farin ciki na hana kaina da ma’aikatana amfana da kwangila - Buhari

Ya ce ba ya bada kwangila kuma babu ruwansa da wanda ya samu kwangilan, muddin sun yi aiki mai kyau a kudi madaidaiciya.

KU KARANTA: Rigimar kungiyar mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3, wasu da dama sun raunata

Shugaban kasan yace an dade an tuhumarsa da abubuwa da yawa amma yan adawarsa ba za su iya tuhumarsa da sata na.

“Ba za ku iya tuhumata da sa taba. Na nada ministoci kuma hakki na kansu. Na gansu a matsayin masu gaskiya ne.”

Ya amsa tambayoyi akan abubuwan da suka tattari suka wanda ya kunshi cewa Musulmai na kokawa kan rashin nada su a mukamai na gwamnati musamman aikin soja.

Shugaban kasa yace wannan aiki na san a da wuyan sha’ani saboda mabiya wasu addinai ma sun kawo masa irin wannan kuka.

Ya yi wadannan bayanai ne ga majalisar koli ta shari’ar Musulunci yayinda suka kawo masa ziyara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel