EFCC ta nemi a dauke shari'ar Shekarau daga kotun Kano saboda dalilan tsaro

EFCC ta nemi a dauke shari'ar Shekarau daga kotun Kano saboda dalilan tsaro

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC ta nemi babban alkalin kotun tarayya ya mayar da sauraron karar sharia'ar tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau zuwa wata jiha saboda tsaro.

A cewar mai magana da yawun EFCC, Mr Wilson Uwujaren, ya bukaci wannan canji ne saboda irin hatsaniya da zanga-zanga da jami'an hukumar suka fuskanta a shar'ar da aka gudanar cikin kwanakin nan.

Ojogbane ya sanar da kotu cewa lauyoyi masu tuhuma sun shigar da bukatar neman a mayar da cigaba da saurarn karar zuwa wata kotun amma ba a Kano ba.

Saboda tsaro: Shari'ar su Shakarau za ta bar Kano zuwa Abuja

Saboda tsaro: Shari'ar su Shakarau za ta bar Kano zuwa Abuja

Sai dai lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma sun bukaci kotun tayi watsi da bukatar ta lauyoyin EFCC inda suka bukaci alkalin da ya yi watsi da bukatar da EFCC ta shigar.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun ci mutunci tsohuwar minista a kofar fadar shugaban Kasa, kalli hotuna

A halin yanzu dai bangarorin biyu suna jiran hukuncin da alkali zai yanke a kan lamarin.

Kazalika, lauyoyin EFCC sun bukaci a dakatar da sauraron karar har sai lokacin da babban alkalin ya yanke hukunci a kan bukatar da suka shigar na neman mayar da shari'ar zuwa wata jiha.

Justice Abubakar ya amince da bukatar dage sauraron karar inda ya ce za'a cigaba da sauraron karar a ranar 18 ga watan Oktoba indan kotun ba ta amince da bukatar mayar da shari'ar wata jiha ba.

Sai dai idan kotun ta amince da mayar da shari'ar zuwa wata jiha, za'a fara sauraron karar tun daga fari.

An gurfanar da Shekarau ne tare da wasu mutane biyu, Aminu Bashir Wali da Mansur Ahmed gaban Justice Zainab Bage Abubakar inda ake tuhumar su da makirci tare da karkatar da kudi har naira 950 miliyan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel